Ahmad Umar

Ahmad Umar My name is Ahmad Umar Baba Falkejo
I'm from Kumo,Gombe Nigeria.

Ramadaniyyat: 1446 [19]‎Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa Manzon Allah‎4.0. Taƙaitaccen Tarihin Masu Ƙaryata Hadisai‎4.5. Was...
20/03/2025

Ramadaniyyat: 1446 [19]‎

Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa Manzon Allah

‎4.0. Taƙaitaccen Tarihin Masu Ƙaryata Hadisai

4.5. Wasu Daga Cikin Jagororin Wannan Fitina: (4)‎

Ci gaba…‎

‎4. Alhafiz Aslam Jirajburi: Haifaffen yakin Azamgrah na ƙasar Indiya. ‎An haife shi a shekara ta 1880. Ya haddace Alƙur'ani yana ɗan shekara tara, ‎saboda haka ne ake masa laƙabi da Alhafiz. Ya karanci harshen Farisanci ‎wanda shi ne yaren koyon addini a lokacin. Sannan ya karanci ilimin lissafi ‎da harshen Ingilishi da harshen Larabci. Bai taɓa shiga wata makaranta ta ‎zamani ba, ballantana ya yi karatun Jami'a, to amma saboda tsananin yadda ‎yake son karance-karance sai ga shi ya kai wani babban matsayi a karatu.‎

Alhafiz Aslam ya zama marubuci a wata jarida mai suna (Baisa) wadda ‎take fitowa kullum a garin Lahore. Wannan ne ma ya sa aka san shi a duk ‎faɗin yankin Indiya. Sannan ya zama malami mai koyarwa a makarantar ‎sakandare, inda ya koyar da harshen Farisanci da Larabci. Sannan a shekara ta ‎‎1912 ya zama mai tsaron ɗakin karatu (Librarian) a wannan makaranta wadda ‎daga bisani aka ɗaga likkafarta ta zama Jami'ar Musulunci inda ya zama mai ‎koyar da harshen Larabci da Farisanci a cikinta. ‎
Sai dai kuma bai daɗe a wannan jami'a ba sai ya koma da koyarwa a ‎Jami'ar Milliya ta Musulunci.‎

Abin da kuwa ya jawo Alhafiz Aslam faɗawa cikin aƙidar "'yan ‎Alƙur'ani zalla" shi ne mas'alar rabon gado, yayin da ya karanta hukunci mai ‎nuna cewa, ɗan ɗa yana hana baffansa watau ɗan'uwan mahaifinsa gadon ‎dukiyar kakansa. Sai wannan hukunci ya taɓa masa zuciya, har ma ya ce, ya ‎duba duk littattafan ilimin rabon gado bai samu wanda ya dace da ra'ayinsa ‎ba, sai Alƙur'ni kaɗai ya goyi bayan ra'ayinsa, don haka ya saɓa wa wancan ‎hukunci.‎

Alhafiz Aslam ya sami ƙulla kyakkyawar alaƙa da Ahmaduddin, ya ‎kuma tasirantu da ra'ayoyinsa na ƙaryata hadisan Manzon Allah (SAW), har ‎ma ya fassara littafinsa "Mu'ujizar Alƙur'ni" zuwa harshen Larabci, ya kuma ‎yaɗa shi cikin ƙasashen Larabawa.‎

Alhafiz Aslam ya rubuta littafin "Mahjub al-Irsi" inda ya yi kakkausan ‎s**a a kan hukunce-hukuncen Muslunci da s**a danganci gado. Hakanan ‎kuma ya ɗosani wani ɓangare na ra'ayin 'yan gurguzu, wato na cewa, duk ƙasa ‎mallakin gwamnati ce.‎

Alhafiz Aslam ya yi rubuce-rubuce masu yawa, ya kuma taɓo ‎ɓangarori daban-daban. Ya yi rubutu a kan tarihin Musulunci da ɓangare ‎Alƙur'ani da na Aƙida da sauransu. Kana iya cewa a cikin tafiyar masu ‎ƙaryata hadisai kakaf, shi ne mutum na biyu bayan Barwiz, saboda yawan ‎littattafan da ya rubuta don yaɗa wannan gurɓatacciyar aƙida.‎

Bayan kafa ƙasar Pakistan a shekara ta 1947 sai Alhafiz Aslam ya amsa ‎gayyatar almajirinsa Barwiz, ya yi hijira zuwa Pakistan. To amma kuma bai ‎daɗe a wannan ƙasa ba, sai ya sake tattara nasa ya nasa ya koma ƙasarsa ta ‎Indiya inda a nan Allah (SAW) ya yi masa rasuwa a ranar 28 ga watan ‎Disamba, shekara ta 1955 yana kimanin ɗan shekara 75 da haihuwa.‎

Za mu ci gaba in sha Allah…
Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo ✍🏻

19/03/2025

Ramadaniyyat: 1446 [18]‎

Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa Manzon Allah

‎4.0. Taƙaitaccen Tarihin Masu Ƙaryata Hadisai

‎4.5. Wasu Daga Cikin Jagororin Wannan Fitina: (3)‎

Ci gaba…‎

‎3. Ahmaduddin Amristari: ɗaya ne daga cikin jigajigen 'yan ƙungiyar ‎‎"Alƙur'ani Zalla". An haife shi a shekara ta 1861, a ƙauyen Amristar da ke ‎jahar Punjab, arewa maso yammacin Indiya. Ya fara karatunsa na addini a ‎wurin mahaifinsa Alkhawaja Muhammad. Daga bisani a ka sanya shi a ‎Makarantan 'yan mishan inda ya yi karatun Bile da ilimin zamani. ‎

Sannan bayan gama wannan karatu, sai ya shiga makarantar Islamiyya ‎ta gaba da Firamare. Daga nan kuma bai ƙara ci gaba da karatu ba. To amma ‎kuma saboda karance-karancensa ya yi suna har ma aka ɗauke shi koyarwa a ‎wata makarantar Islamiyya, a ƙauyensu Amristar. ‎

Bayan ya gama aiki a wannan makaranta ne, sai ya shiga harkar ‎karantar da Alƙur'ani inda ya samu shuhura a ilahirin yankin Indiya.‎

Ahmaduddin ya ƙware wajen magana da yaruka daban-daban, ciki har ‎da harshen Larabci da na Farisanci da harshen Urdu da kuma yaren Punjab, ‎wanda shi ne yarensa na haihuwa. Sannan ya ƙware a ilimin tattalin arzuki da ‎na Tarihi da ilimin labarin ƙasa da lissafi da ilimin Falaki da sauran ilimomin ‎Musulunci.‎

Ahamaduddin ya yi amfani da ra'ayoyin Ahmad Khan, amma bai ɗauke ‎su a matsayin jigon kafa nasa ra'ayoyin ba, domin ganin irin s**an da s**a ‎sha a wajen malaman addini.‎

Ya kuma samu kyakkyawar alaƙa da Abudullahi al-Jakralawi, lokacin ‎da shi al-Jakralawi yake tsaka da tallata da'awarsa ta ƙaryata hadisan Manzon ‎Allah (SAW) a shekara ta 1902. ‎

Ahmaduddin ya kasance a duk lokacin da ya samu hutun makaratar ‎Islamiyya inda yake koyarwa, sai ya kai wa al-Jakralawi ziyara. Sukan zauna ‎tare su tattauna matsalolin addini bisa irin fahimtarsu ta ƙaryata hadisai, ‎s**an kuma ƙaru da juna.‎

Lokacin da al-Jakralawi ya saki littafinsa mai suna "Sallar Alƙur'ani",
‎Ahmaduddin ya kai masa ziyara inda ya ja hankalinsa cewa, ya guji yaɗa ‎littattafai irin waɗannan a halin da ake ciki. Suna tsaka da tattaunawa ne ‎lokacin sallar La'asar ya yi, sai Ahmaduddin ya yi salla irin sallar al-‎Jakralawi, sai ya ce masa: "Ya ya kake nuna rashin yardarka da littafin, kuma ‎kake yin irin sallar da yake koyarwa?" Sai Ahmaduddin ya amsa masa da ‎cewa: "Ai ban ce sallar ɓatacciya ce ba, amma ina ga bai dace a raba kan ‎Musulmi ba".‎

Alkhawaja Ahmaduddin ya kafa ƙungiyarsa a shekara ta 1926 ya sanya ‎mata suna "Ummatun Muslimah", kuma mutane da dama s**a riƙa rigegeniya ‎wajen shiga cikinta. Sannan ya kafa wata mujalla mai suna "Balag" wadda ta ‎ɗauki gabarin yaɗa da'awar wannan ƙungiya.‎

‎'Yan ƙungiyar "Ummatun Muslima" sun tashi tsaye wajen buga ‎littattafai masu ɗauke da ra'ayoyinsu, s**a riƙa yaɗa su ko'ina da aika wa ‎mutane har gidajensu, al'amarin da ya ja mutane da dama s**a riƙa faɗa wa ‎cikin wannan mummunar aƙida.‎

Sauƙin hali da Ahmaduddin yake da shi ya ja mutane masu yawa zuwa ‎ga karɓar rayoyinsa, cikinsu har da manyan 'yan kasuwa da mutane masu ‎basira.‎

Ahamaduddin ya fito ƙarara yana s**an tsarin rabon gado na Musulmi, ‎inda ya riƙa kira cewa, lalle a wadatu da iya abin da Alƙur'ani ya ambata na ‎hukunce-hukuncen rabon gado, kada a yi amafani da abin da ya zo a cikin ‎hadisan Annabi (SAW), don haka yana ganin jika na ɓangaren ɗa namiji zai ‎iya cin gado koda kuwa ɗan yana nan da rai. Sannan ya wajabta wa kowane ‎mai rasuwa dole ne ya yi wa magadansa wasiyya. Hakanan yana ga mutum ‎kowane irin addini yake bi zai iya cin gadon ɗan'uwansa Musulmi. Da sauran ‎miyagun ra'ayoyinsa waɗanda s**a saɓa wa ijma'in Musulmin duniya.‎

Ahmaduddin ya yi rubuce-rubuce masu yawa bisa fahimtarsa ta ‎‎"Alƙur'ani zalla". Ya rubuta tafsirin Alƙur'ani cikin sifili bakwai.‎

Ahmaduddin ya rasu ranar Talata 2 ga watan Yuni, shekara ta 1936.‎

Za mu ci gaba in sha Allah….‎
Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo ✍🏻

Ramadaniyyat: 1446 [17]‎Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa Manzon Allah‎4.0. Taƙaitaccen Tarihin Masu Ƙaryata Hadisai‎4.5. Was...
17/03/2025

Ramadaniyyat: 1446 [17]‎

Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa Manzon Allah

4.0. Taƙaitaccen Tarihin Masu Ƙaryata Hadisai

4.5. Wasu Daga Cikin Jagororin Wannan Fitina: (2)‎

Ci gaba…‎

2. Abdullahi al-Jakralawi haiffaffen garin Punjab na ƙasar Indiya, ‎sannan mazaunin garin Lahore da ke ƙasar Pakistan, shi ne mutumin da ya ‎kafa ƙungiya ta farko ta 'yan 'Alƙur'ni zalla', ya sanya mata suna: "Ahuluz ‎Zikri wal ƙur'an", ya kuma ƙaryata duk hadisan Annabi (SAW) kakaf.‎

Ya auri mata biyu. Ta farko a lokacin samartakarsa, wadda kuma ta ‎Haifa masa 'ya'ya biyu, su ne: Ibrahimu da Alƙali Muhammadu Isa. Shi ‎Ibrahim bai gamsu da ra'ayoyin mahaifinsa ba, don haka, ya nisanta kansa da ‎shi. Hakan ne ma ya sanya ubansa ya raba gari da shi, ya kuma haramta masa ‎ya ci gadonsa bayan mutuwarsa. Ibrahimu ya rasu a sherkar ta 1918.‎

Amma shi Alƙali Muhammadu Isa ya zaɓi ya bi tafarkin mahaifinsa, ya ‎kuma zama mai taimakonsa wajen yaɗa mummunar aƙidarsa, to sai dai kuma ‎shi Allah bai yi masa baiwar hazaƙa ba, don haka bai je ko'ina ba ‎tauraruwarsa ta dusashe.‎

Matar al-Jakralawi ta biyu ita ce, tubabbiyar bayahudiyar Amuruka ɗin ‎nan mashahuriya mai suna Maryam Jamila wadda ta Musulunta a ƙasar ‎Pakistan, ta kuma auri Abullahi al-Jakralawi, duk kuwa da tazarar shekaru da ‎ke tsakaninsu. Ya aure ta a lokacin da ya tasamma shekara tamanin a duniya. ‎Ita ma Maryam Jamila ta rungumi aƙidar mijinta matuƙa, ta kuma sadaukar da ‎rayuwarta ga mijinta sosai, kai har ma ana ganin ba domin ita mace ce ba, to ‎da ita ce za ta gaji mijinta wajen jagorancin ƙungiyar Alhluz Zikri. Ta rasu a ‎shekarar 1978.‎

Abdullahi al-Jakralawi ya fara karatun addini a hannun mahaifinsa, ‎sannan ya shiga makarantu masu zaman kansu, daga bisani ya bar garin ‎Punjab zuwa garin Delhi inda ya yi karatun ilimin hadisi a wajen babban ‎malamin hadisin nan Sheikh Naziru Husaini, to amma fa tun lokacin da yake ‎karatu a gabansa, Sheikh Nazir ya fara ganin take-taken fanɗara a tare da shi.‎

Abdullahi al-Jakralawi ya fara tsunduma cikin wannan hanyar ɓatan ne ‎bayan wata tattaunawa da ya yi da wani baffansa mai suna Alƙali ƙamaruddin ‎al-Hanafi, wanda ya riƙa bijiro masa wasu hadisai da ya gaza fahimtar su, sai ‎kawai ya buɗi baki ya ce: "Alƙur'ani ne kaɗai littafin da aka yi wa ‎Muhammadu (SAW) wahayinsa. Duk wani abu wanda ba Alƙur'ani ba, to ba ‎zai taɓa zama wahayi ba". ‎

Daga nan ya fara rubutun littafinsa na tafsirin Alƙur'ani bisa aƙidarsa.‎

Abdullahi al-Jakralawi yana magana da harsuna biyu ƙwarara: Harshen ‎Larabci da na Urdu. Yana da ilimi mai zurfi cikin harshen Larabci: Ya ƙware a ‎ilimin Nahawu da Sarfu da Balaga da kuma Adabin Larabci. Ya yi rubuce-‎rubuce masu ɗimbin yawa, yana da kuma yawan jayayya tare da wulaƙanta ‎litttafan Musulunci, bai kuma san wani abu kara ba ko kaɗan.‎

Ya yi rubutu a kan 'Fassarar Alƙur'ani da Alƙur'ani, ya kuma rubuta ‎‎"Sallar Alƙur'ani" da "Zakka da Sadaka Kamar Yadda Take a Cikin Ayoyin ‎Alƙur'ani", da sauran rubuce-rubuce a cikin harshen Urdu.‎

Wasu marubuta sun tabbatar da cewa wannan malami yana ɗaya daga ‎cikin malaman da s**a faɗa cikin komar 'yan mulkin mallaka, kuma ‎gwamnatin ƙasar Birtaniya ta yi amfani da shi wajen kawo wa Musulmin ‎Indiya ruɗani a cikin sha'anin addininsu. Don haka ya fito yana kira da babbar ‎murya cewa, lalle Musulmi su yi watsi da hadisan Annabi (SAW) domin ‎dukkansu ƙarya ne ba gaskiya ba.‎

'Yan mulkin mallaka sun riƙa tura masa kuɗaɗe waɗanda ya riƙa ‎amfani da su wajen biyan masu fassara masa bayanansa da littattafansa zuwa ‎harshen Ingilishi.‎

Abdullahi al-Jakralawi ya kafa babbar cibiyar da'awarsa a garin Lahore ‎na ƙasar Pakistan. Lahore gari ne na ilimi da malamai. Daga wannan gari ne ‎ya riƙa yaɗa ɓarnarsa zuwa garuruwan Musulmi daban-daban.‎

To amma cikin hikimar Allah sai aka samu wata mujalla ta Musulmi ‎Ahlussunna mai suna "Isha'atus Sunna" wadda ta yi bincike a kan miyagun ‎ra'ayoyin wannan malami, sannan ta tattara su ta buga su, ta kuma aika da su ‎zuwa ga malaman addini inda ta nemi su bayyana matsayar addini game da ‎waɗannan ra'ayoyi da kuma hukuncin wanda ya yarda da su: shin za a ci gaba ‎da ɗaukar sa a matsayin Musulmi ko kuma ya fita daga da'irar Musulunci?‎

Mafi yawan Malamai na yankin Indiya: ƙasar Pakistan da Indiya da ‎Bangladesh, dukkansu sun ba da fatawa da cewa, mai irin waɗannan ra'ayoyi ‎‎(watau Abullahi al-Jakralawi) ya kafirta. Mujallar "Isha'atus Sunna" kuwa ta ‎buga bayani a kan wannan fatawa tare da sa hannun duk malaman addini ‎waɗanda s**a bayar da fatawar kafircin al-Jakralawi tare da ba da tabbacin ‎cewa ya bar Musulunci.‎

Amma kuma duk da fitowar wannan fatawa ta malamai, Abullahi al-Jakralawi ‎bai janye miyagun ra'ayoyinsa ba, ballantana ya tuba zuwa ga Allah. A'a a ‎madadin haka sai ya ƙara ƙaimi wajen ci gaba da yaɗa mummunar aƙidarsa da ‎ɓatar da al'umma har zuwa lokacin da mutuwa ta riske shi, ya koma ga Allah ‎mahaliccinsa a shekara ta 1914.‎

Za mu ci gaba in sha Allah….. ‎
Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo ✍🏻

17/03/2025

Allah kasa muna da rabo a aljannah 🤲🙏

Allah ya qarama lpy🤲
17/03/2025

Allah ya qarama lpy🤲

08/03/2025

Ramadaniyyat: 1446 [8]‎

Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa Manzon Allah

‎3.0. Sunna a Mahangar Alƙur'ani Mai Girma

Ci gaba…..‎

‎3.2. Allah (SWT) ya Ɗora wa Annabi (SAW) Nauyin Bayanin ‎Ma'anonin Alƙur'ani Mai Girma: (2)‎

A ci gaba da ambaton ayoyin Alƙur'ani da s**a bayyana cewa, ‎Allah (SAW) ya ɗora wa Annabi (SAW) nauyin bayanin duk abin da ‎yake buƙatar bayani a cikin Alƙur'ani mai girma.‎

Aya ta uku: Allah yana cewa:‎

‎(Ba Mu taɓa aiko wani manzo ba kuwa sai da harshen mutanensa ‎don ya yi musu bayani; sannan Allah Yana ɓatar da wanda ya ga ‎dama, ya kuma shiryar da wanda ya ga dama. Shi ne kuwa ‎Mabuwayi, Mai hikima) [Ibrahim, aya ta 4].‎

A wannan aya Allah (SWT) ya bayyana rahma da baiwa da ya yi ‎wa bayinsa ta aiko musu da manzanni, kowane manzo ya riƙa magana ‎da harshen mutanensa da aka aiko shi wajensu, domin su samu damar yi ‎musu bayanin saƙon da aka aiko su da shi, su kuma mutanen su iya ‎fahimtar bayanin da manzanninsu za su yi musu.‎

A nan ya bayyana a fili Allah ya nuna cewa, yana daga cikin aikin ‎kowane manzo da Allah ya taɓa aiko wa, yi wa mutanensa bayanin ‎saƙon da ya zo musu da shi. Annabi Muhammadu ɗaya ne daga cikin ‎waɗannan manzonni, saboda haka ya yi wa al'ummarsa bayanin saƙon ‎Allah da ya saukar masa watau Alƙur'ani da harshen da mutanensa suke ‎magana da shi watau larabci. Wannan bayanin kuwa su ne tabbatattun ‎hadisansa waɗanda suke ɗauke da bayanin sunnoninsa.‎‏ ‏‎ Don haka ‎ƙaryata hadisan Annabi (SAW) daidai yake da ƙaryata faɗin Allah cewa, ‎kowane annabi yana yi wa mutanensa bayanin abin da aka aiko shi da ‎shi na wahayi.‎

Aya ta huɗu: Allah yana cewa:‎

(Allah ya ce da Annabinsa): Kada ka motsa harshenka da shi ‎‎(Alƙur’ani) don gaggauta (karanta) shi. Lalle tattara shi (a ‎zuciyarka) da karanta shi yana kanmu. Saboda haka idan Muka ‎karanta (maka) shi sai ka bi karatunsa. Sannan kuma bayaninsa yana ‎kanmu). [Al-kiyama, aya ta 16-19]. ‎

A waɗannan ayoyi Allah (SWT) ya bayyana tsananin kwaɗayin Manzonsa ‎‎(SAW) wajen sa

07/03/2025

Ramadaniyyat: 1446 [7]‎

Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa Manzon Allah

3.0. Sunna a Mahangar Alƙur'ani Mai Girma

Ci gaba…..‎

3.2. Allah (SWT) ya Ɗora wa Annabi (SAW) Nauyin Bayanin ‎Ma'anonin Alƙur'ani Mai Girma:‎

Ayoyin Alƙur'ani sun bayyana cewa, Allah (SAW) ya ɗora wa ‎Annabi (SAW) nauyin bayanin duk abin da yake buƙatar bayani a cikin ‎Alƙur'ani mai girma. ‎

Aya ta farko: Allah (SAW) yana cewa: ‎

‎(Mun kuma saukar maka da Alƙur’ani don ka yi wa mutane ‎bayanin abin da aka saukar musu ko sa yi tunani). [Nahl: aya ta 44].‎

A wannan aya Allah (SAW) ya tabbatar da cewa, shi ne ya saukar da ‎Alƙur’ani ga Manzon Allah (SAW) domin ya zamanto wa’azi da tunatarwa ga ‎mutane, kuma ya ɗora wa Annabi (SAW) nauyin yi musu bayani filla-filla na ‎abubuwan da ya ƙunsa masu buƙatar ƙarin bayani, don mutane su yi tunani su ‎fahimci abin da ya zo da shi su wa’azantu.‎

A nan Allah (SWT) ya bayyana abin da ya saukar wa Annabi ‎‎(SAW) wato Alƙur'ani wanda ya kira "Zikr", sannan ya bayyana Mazon ‎Allah (SAW) a matsayin wanda zai yi bayanin abin da yake buƙatar ‎bayani daga cikin Alƙur'ani.‎

A nan Ayar ta ƙunshi abubuwa biyu: 1. Alƙur'ani, 2. Bayin ‎alƙur'ani wanda aka ɗora alhakin gabatar da shi a kan Annabi (SAW). ‎

Wannan ƙarara ya tabbatar mana da cewa, akwai Saukakken littafi, ‎shi ne Alƙur'ani; akwai kuma bayanin da Annabi (SAW) yake yi na shi ‎Alƙur'anin. To waɗannan bayanai su ne tabbatattun hadisansa wanda ‎s**a ƙunsi sunnoninsa, na maganganunsa ko ayyukansa.‎

Dole ne kowane Musulmi a ko'ina, a kuma kowane zamani, ya ‎rungumi Alƙur'ani tare da waɗannan bayanai na Manzon Allah (SAW) ‎ya kuma yi aiki da su. ‎

Idan kuwa haka ne, to wannan yana nuna lalle Allah (SAW) zai ‎tsare waɗannan bayanin ga al'ummomi masu zuwa, domin hujjarsa ta ‎tsayu a kan bayinsa har zuwa tashin alƙiyama.‎
Saboda haka wannan aya ta tabbatar da abubuwa kamar haka:‎

1. Saukar da Alƙur'ani ga Annabi (SAW).‎

2. Jiɓinta wa Annabi (SAW) alhakin yi wa mutane bayanin ‎alƙur'ani, ta hanyar karantar

07/03/2025

Ramadaniyyat: 1446 [6]‎

Alƙur'ani Zalla ko Bijire wa wa Manzon Allah

3.0. Sunna a Mahangar Alƙur'ani Mai Girma

‎3.1. Sunna Wahayi ce Daga Allah Kamar Alƙur'ani: (3)‎

Ci gaba….‎

Ci gaba da bayanin dalilai daga Alƙur'ani masu tabbatar da cewa, ‎annabawa, Allah yakan yi musu wahayi iri biyu, akwai na littafi, akwai ‎kuma wahayin da ba ya cikin littafin (Sunna):‎

Misali Na biyu: Annabi Ibrahim (AS):‎

Allah yana cewa:‎

‎(…To haƙiƙa Mun bai wa zurriyar gidan Ibrahimu Littafi da kuma ‎hikima, kuma Mun ba su wani mulki mai girma). [Nisa'i, aya ta 54].‎

A wannan ayar Allah (SWT) ƙarara ya bayyana cewa, ya ba wa ‎zurriyar Annabi Ibrahim – har da shi kansa Ibrahimu ɗin- annabta, ya ‎kuma ba su littafi da hikima. Hikima su ne bayanan wasu hukunce –‎hukunce da ya riƙa saukar musu da wahayinsu bayan littafi da ya ba su. ‎

Wannan yana tabbatar da cewa, sunna wahayi ne daga Allah, ‎kamar yadda littafin da Allah ya ba wa kowane annabi yake wahayi.‎

Misali na uku, Annabi Musa (AS):‎

Allah (SWT) ya karrama Annabi Musa (AS) da annabta a kan ‎hanyarsa ta dawowa daga garin Madyana. Allah ya yi masa wahayi inda ‎ya ba shi umarni da ya tafi zuwa Fir'auna da mutanensa ya kira su zuwa ‎ga bautar Allah shi kaɗai, sannan ya umarce su da su saki Banu Isra'ila ‎da suke riƙe da su. Amma a duk wannan lokaci, Allah bai ba wa Annabi ‎Musa (AS) littafin Attaura ba, domin ba a saukar da Attaura ba sai ‎bayan an hallakar da Fir'auna da mutanensa. Annabi Musa (AS) ya ‎tsayar wa da Fir'auna da Hamana da ƙaruna da mutanensu hujja da ‎wahayin sunna, ba da abin da yake rubuce a cikin Attaura ba.‎

Allah yana cewa: ‎

‎(Haƙiƙa kuma Mun bai wa Musa littafin (Attaura) bayan Mun ‎hallaka al’ummu na farko don izina ga mutane da shiriya da rahama ‎ko sa wa’azantu).[al-ƙasas, aya ta 43]. ‎

A nan Allah ya nuna cewa, bayan saukar da Attaura, Allah bai sake ‎hallakar da wata al'umma a bayan ƙasa hallakarwa ta gaba ɗaya ba.‎
Allah ya ba wa Annabi Musa littafin Attaura ne lokacin da suke ‎rayuwar ɗimuwa

Address

Along Sagak Kumo
Kumo

Telephone

+2347047390861

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ahmad Umar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ahmad Umar:

Share