MTA

MTA ON LINE REGISTRATION WILL START SOON I N SHA ALLAH

21/02/2026
21/02/2026

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa INEC da hukumomin tsaro kan yadda s**a gudanar da zaben cike gurbi cikin lumana da tsari a jihar Kano.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, gwamnan ya bayyana zaben a matsayin wani babban ci gaba a tafiyar dimokuradiyyar jihar, yana mai cewa yanayin natsuwa da aka samu a rumfunan zabe ya nuna yadda al’umma s**a kara fahimtar siyasa da kuma ingancin tsare-tsaren tsaro da aka shimfida.

Gwamna Yusuf ya kuma yabawa al’ummar mazabun Kano Municipal da Ungogo na majalisar dokokin jiha bisa hadin kai, da’a da kuma jajircewarsu wajen fitowa cikin lumana domin kada kuri’unsu. Haka kuma ya jinjinawa jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki, musamman mambobin APC duk wani abu da zai iya kawo cikas.

Me za ku ce?.

02/06/2024
02/06/2024
02/06/2024

Ba bu Sasantawa Kan Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi – Doguwa

Shugaban kwamitin kula da harkokin man fetur na Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ya ce batun samar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi a kasar nan shi ne babban fifiko.

Doguwa ya shaida wa manema labarai a Kano ranar Asabar cewa: “Rashin zaman lafiya, talauci, da rashin ci gaban da ake fama da shi a yau duk sakamakon rashin ayyukan yi ne na kananan hukumomin kasar nan.”

Doguwa, wanda ya bayyana a cikin Wata rigar basaraken gargajiya, ya ce: “Na kasance Sardauna Doguwa ne, domin a iya sanina, rigimar da ke tattare da rusa masarautun (Kano) har yanzu batu ne na shari’a. Ya bayyana cewa ita ma wannan majalisar ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an amince da kudurin dokar man fetur ya zama doka, kuma a yau, dangane da wannan fanni, Nijeriya na tafiya da kafadarta a tsakanin kasashen duniya.”

Da yake tunawa a yau kasar ta fi kyau saboda wasu kudirori da dama da aka zartar da su a matsayin doka, ya ce:

“Saboda haka, ya kamata mu wuce gona da iri domin ganin an samu ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi. Don haka ne nake son shugaban majalisar da kansa ya jagoranci kwamitin duba kundin tsarin mulkin kasar domin mu yi sihiri tare.

"Ina tabbatar muku da cewa idan kananan hukumomi s**a sami 'yancin cin gashin kansu, 'yan Najeriya za su sake kwana da idanunsu a rufe kuma su zaga ko'ina ba tare da fargabar an yi musu fyade ko a dauke su ba."

Daga: Abbas Yakubu Yaura

02/06/2024

*INFORMATION!!!*
I'm directed to inform you, no movement of commercial tricycle (keke) effective from tomorrow 2/6/2024 7am to 10am as regard to nationwide strike by organized labour,

Pls endeavor to adhere strictly to directive to avoid unnecessary blaming

You can buy your fuel today against tomorrow as they will be a total shutdown of petrol stations throughout tomorrow.

Address

No6Bishop Street Opperluggere Jimeta
Yola

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MTA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share